Home Labarai Majalisar Dattawa ta fara bincike kan kisan ‘yan Nijeriya 250 a Habasha

Majalisar Dattawa ta fara bincike kan kisan ‘yan Nijeriya 250 a Habasha

by Muhsin Tasiu Yau

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Majalisar Dattijai ta matsa ƙaimi domin gudanar da bincike kan kashe-kashe da ɗaure ‘yan Nijeriya sama da 250 a ƙasar Habasha.

Hakan ya biyo bayan wani ƙudiri mai taken, ‘Akwai buƙatar a gaggauta bincike kan kashe-kashen da aka yi wa ‘yan Nijeriya sama da 250 a ƙasar Habasha ba bisa ƙa’ida ba, wanda shugaban marasa rinjaye, Sanata Simon Mwadkwon, ɗan Jam’iyyar Peoples Democratic Party, (PDP) mai wakiltar Filato ta Arewa, da Sanata Victor suka ɗauki nauyi.

Da yake gabatar da ƙudirin, Mwadkwon ya buƙaci majalisar dattijai da ta umurci kwamitocin ƙasashen waje da su haɗa kai da gwamnatin tarayya domin kafa kwamitin gaggawa da zai ziyarci jamhuriyar Habasha da nufin binciken abubuwan da ke faruwa ga ‘yan Nijeriya a ƙasashen ƙetare.

Ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta umurtar ofishin jakadancin ƙasar Habasha da ya haɗa kai da tawagar kwamitocin majalisar dattawa kan ƙasashen waje domin samar da dawwamammiyar mafita kan matsalolin da ‘yan Nijeriya ke fuskanta.

Mwadkwon ya ce, “bidiyon da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta na yanar gizo ya nuna cewa ‘yan Nijeriya na tsare a gidan yari mafi girma na ƙasar Habasha kuma suna cikin haɗari mai tsanani wanda ya buƙaci a gaggauta shiga tsakani da kuma yin cikakken bincike kan munanan ayyukan.”

Ya koka da cewa hakan na faruwa duk da kiraye-kirayen haɗin kai tsakanin ƙasashen duniya.

Related Posts

Leave a Comment