Home Labarai ZAMAN MAJALISAR ZARTARWA NA JIHAR KANO

ZAMAN MAJALISAR ZARTARWA NA JIHAR KANO

by masta

Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida), ya ci gaba da jagorantar zaman Majalisar Zartarwa ta jihar, wanda ake gudanarwa a Gidan Gwamnati, Kwankwasiyya City.

1. Rahoton Aikin Hajji 2025
– Hukumar Jindadin Alhazai ta Jihar Kano ta gabatar da cikakken rahoto kan yadda aikin Hajjin bana ya gudana, tare da bayyana nasarorin da aka samu, matsalolin da aka fuskanta, da kuma shawarwari don inganta gudanarwar shekaru masu zuwa.

2. Ayyukan Gine-gine da Tsare-tsare na 2025
– Ma’aikatar Ayyuka ta gabatar da karin bayani kan ci gaban ayyukan gine-gine, musamman titunan 5km a kananan hukumomi, gyare-gyaren manyan hanyoyi kamar Jaba–Gayawa, Zungeru, Bompai da sauran su, tare da sabbin kwangiloli da ake shirin kaddamarwa.

3. Ilimi da Lafiya
– Ma’aikatar Ilimi ta gabatar da rahoto kan sabbin makarantun da aka kammala gyarawa da kuma ajujuwan da ake ginawa a fadin jihar.
– Ma’aikatar Lafiya ta bayyana sabbin kayan aiki da aka shigar a asibitoci, musamman sabuwar PSA Oxygen Plant da aka kaddamar a jiya domin inganta kula da lafiya.

4. Shirin Gina Sabbin Garuruwa
– An tattauna kan ci gaban ayyukan raya sabbin birane na Kwankwasiyya, Amana da Bandirawo Cities, da suka haɗa da tsarin samar da hasken wuta, hanyoyi, ruwan sha da sauran abubuwan more rayuwa.

5. Batun Tattalin Arziki da Ayyukan Yi
– An gabatar da karin bayani kan shirye-shiryen bunkasa masana’antu da kasuwanci, tallafawa matasa da kayan aiki, da kuma ci gaba da shirin Green Kano na dasa miliyoyin bishiyoyi don inganta muhalli da tattalin arzikin al’umma.

Zaman majalisar na yau na da matuƙar muhimmanci kasancewar ya kunshi:
• Rahotanni daga hukumomi da ma’aikatun gwamnati daban-daban,
• Yanke sabbin shirye-shirye da suka shafi ci gaban al’umma,
• Samar da ayyukan yi da habaka tattalin arziki,
• Raya bangaren ilimi da lafiya.

A takaice, wannan zaman ya nuni da yadda gwamnatin Abba Kabir Yusuf ke ci gaba da aiwatar da manufofinta na “Abba Gida-Gida – Gwamnati Mai Amfanar Jama’a.”

Related Posts

Leave a Comment