Home Labarai Rundunar ‘Yan saandar jihar Katsina za ta rubanya tsaro yayin gudanar da zagayen mauludi

Rundunar ‘Yan saandar jihar Katsina za ta rubanya tsaro yayin gudanar da zagayen mauludi

by masta

Rundunar ‘yan sanda ta kasa reshen Jihar Katsina zata rubanya jami’anta, a wajen zagayen maulidi na bana a Jihar domin tabbatar da tsaro yayin gudanar da zagayen.

Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Katsina CP. Bello Shehu ya bayyana haka ranar laraba 10/9/2025, a ofishinsa dake hedikwatar hukumar dake cikin garin Katsina.Yayin da ya amshi bakuncin kwamitin kula da zagayen maulidi na Jihar karkashin ofishin mai taimaka ma Gwamna na musamman akan harkokin Darika Malam Muhammed Mahi.

CP. Bello Shehu ya ci gaba da yaba ma kwamitin akan kokarin da yake na tsabtace harkar zagayen maulidin na hana shigar kauraye masu tada hayaniya da masu harkar shaye, shaye. Rundunar yan sanda ta Jihar Katsina zata rubanya jami’anta yayin gudanar da zagayen maulidin na bana, domin bada cikakken tsaro, don ganin anyi lafiya an gama lafiya kamar yadda kwamishinan ya bayyana.

Tun da farko da yake gabatar da jawabinsa, mai taimaka ma Gwamnan na musamman akan harkokin Darika Malam Muhammed Mahi ya jinjina ma rundunar ‘yan sandan akan kokarin da ta ke na bada tsaro yayin gudanar da zagayen maulidi duk shekara.

Saboda haka makasudin wannan ziyara domin mu gabatar ma rundunar shirin kwamitin na gudanar da zagayen maulidin bana, domin a samar da tsaro kamar yadda rundunar ta saba duk shekara, don ganin anyi lafiya an gama lafiya.

Malam Muhammed Mahi ya ci gaba da cewa” Wannan kwamitin Gwamnatin da ta gabata ta Rt. Hon. Aminu Bello Masari ta kafa wannan kwamitin domin tsabtace harkar zagayen maulidin kuma da Gwamnatin Malam Dikko Umar Radda tazo ta dabbaka aikin kwamitin.

Sauran tawagar kwamitin sun hada da Sheriff Abba Amadu Rafindadi shugaban kwamitin, Malam Yazidu Aminu Masanawa Sakataren kwamitin. Da dai sauransu

Related Posts

Leave a Comment