Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da sabon umarni ga wani kwamiti na Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) da ya ɗauki matakan gaggawa domin rage tsadar kayan abinci a faɗin Najeriya.
Wannan umarni na zuwa ne a daidai lokacin da ƙorafe-ƙorafe daga al’umma ke ƙaruwa kan yadda tsadar abinci ke ci gaba da ƙaruwa a kasuwanni, duk da irin matakan da gwamnatin tarayya ta gabatar tun bara domin farfaɗo da fannin noma da kuma shigo da kayan abinci daga ƙasashen waje.
A baya, gwamnatin Tinubu ta dakatar da haraji kan shigo da hatsi na tsawon kwanaki 150, ta kuma fitar da dubban ton na hatsi da shinkafa daga ajiyar gwamnati domin sauƙaƙa wa talakawa. Haka zalika, ministocin gwamnati sun sha ikirarin cewa farashin abinci ya fara raguwa, sai dai rahotanni daga ƙasa sun nuna farashi na ci gaba da hawa, inda ma’aunin “Jollof Index” ya nuna tsadar girki ta tashi sama da kashi 150 cikin ɗari a cikin shekara biyu.
Sabon umarnin Shugaba Tinubu yana nuni da cewa gwamnati ba ta gamsu da irin tasirin matakan baya ba, lamarin da ya sanya al’umma jiran ganin irin sabbin dabarun da kwamitin FEC ɗin zai gabatar domin sauƙaƙa wa ‘yan kasa.


