164
Gwamnatin Kano ta ayyana gobe Jumma’a, 12 ga Satumba, 2025 (19 ga Rabi’ul Awwal 1447 AH) a matsayin hutun gwamnati domin bikin Maulidi – zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW).
Gwamnatin ta bukaci ma’aikatan gwamnati, masu zaman kansu, da daukacin al’umma su yi amfani da wannan dama wajen tunawa da koyarwar Annabi (SAW), su zauna lafiya, su kuma roki zaman lafiya da cigaba ga Kano da Najeriya baki ɗaya.
Hakanan, gwamnatin ta taya jama’ar Kano murnar wannan rana mai albarka, tana masu fatan bikin da cike da kwanciyar hankali da albarka.


