Gwamna Raɗɗa ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da yake buɗe taron ƙarama juna sani ga Ma’aikatan Shari’a domin inganta ayyukan su.
Taron wanda ya gudana a ɗakin taro na Babbar Kotun Jiha dake a hanyar Daura.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa, Gwamnatin shi ba zatai ƙasa a gwiwa ba wajen tabbatar da kowace doka da zata kawo inganta harkokin Shari’a ba a Jihar nan.
Ya kumayi kira ga Ɓangaren na Shari’a da a kowane lokaci su kasance masu yin sauri wajen yanke hukunci ga masu laifuka akan lokaci.
Gwamnan ya kuma ƙara kira ga ɓangaren na Shari’a akan su kasance masu rage cunkoso a gidajen yari domin hakan zai inganta lafiyar masu zaman sarƙar dake a gidajen yarin.
Ya kuma ƙara nanata cewa, Gwamnatin shi a shirye take ta kawo wasu dokoki da zasu inganta harkokin ayyukan Shari’a a Jihar nan domin aiwatar da doka da oda a kowanne lokaci.
Itama da take bayani a wajen taron, Kwamishiniyar Harkokin Shari’a ta Jiha, Mai Shari’a Fadila Muhammad Dikko ta bayyana cewa manufar taron ƙarama juna sanin shine domin ƙarfafama Ma’aikatan Shari’ar gwiwa da kuma a tunatar da su akan wasu dabarun ayyukan su dama na zamani.
Mai Shari’a Fadila Muhammad Dikko ta kuma bayyana cewa, daga cikin waɗan da suka gayyata domin halartar taron sun haɗa da ɓangarorin Jami’an Tsaro da suka haɗa da Ƴan Sanda, HISBA, Hana Fasa Ƙwauri, Fice da Shiga, Sojoji, Yan Sandan cikin gida da dai sauran su.
Mai Shari’ar ta kuma godema Gwamna Raɗɗa akan gudummuwar da yake ba ɓangaren Shari’a da sauran dukkan muƙarraban Gwamnatin Jihar.
Rabiatu Sulaiman Kurfi
S.A Digital Media to
Katsina State Governor






