Duk wanda bai ci jarabawar ba zai iya rasa nukaminsa ya koma rike alli
Ma’aikatar Ilimin Firamare da Sakandare ta jihar Katsina a ranar Talata ta sanar da cewa, ana shirin gudanar da jarabawar gwaji ga ɗaukacin shugabanni (Principals) mataimakan shugabannin makarantun sakandire da ke fadin jihar.
Sakamakon jarabawar aka yi a cewar kwamishinan ma’aikatar Hon. Zainab Musawa, zai taimaka wajen naɗa mukamai tare da tabbatar da bin cancanta a makarantu, ta yadda za a inganta kwazo da ingantaccen jagoranci a makarantun.
Hakanan Kwamishiniyar ta karyata rahotannin da kafafen yada labarai suka yada a baya-bayan nan da ke nuna yadda jihar ta samu sakamakon jarabawar NECO ta shekarar 2024
A cewarta, duk da yawan adadin da aka samu, jihar Katsina ta samu matsayi na shida a fadin kasar nan a cikin adadin daliban da suka ci jarrabawar NECO da maki biyar da sama da haka, wadanda suka hada da Mathematics da Ingilishi, inda dalibai 29,633 suka samu wannan muhimmin matsayi.


