Home Labarai Gwamnatin Jihar Sokoto ba ta shiga cikin bayar da kwangilar hakar rijiyoyin burtsatse ba:

Gwamnatin Jihar Sokoto ba ta shiga cikin bayar da kwangilar hakar rijiyoyin burtsatse ba:

by masta

Na samu damar fayyace batun da ke tattare da rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana guda 25 a Karamar Hukumar Wurno. Na yi magana a Goronyo a lokacin kaddamar da gangamin yakin neman zaben APC na Yankin Gabas na Sokoto a gabanin zaben kananan hukumomi mai zuwa.

Ba Gwamnatin Jihar Sokoto ce ta bayar da kwangilar aikin ba. Wannan aiki ne da Bankin Duniya, gwamnatin tarayya da jiha, da kuma aikin ACREsAL suka dauki nauyi tare, da nufin samar da ruwa ga yankunan Munki, Lugu, Wurno, Dinawa, da Marnona.

Ba mu taba shiga cikin tsarin bayar da kwangilar hakar sababbin rijiyoyin burtsatse ba. Batun gyaran rijiyoyin burtsatse a Wurno ma be taso ba saboda ba za ka iya gyara abin da ba ya wanzuwa ba. Ba a taba hakar rijiyoyin burtsatse a wadannan wurare kafin zuwanmu kan mulki ba, shi ya sa muka dage kan hakar sababbin rijiyoyin burtsatse ga wadannan al’ummomi.

Gwamnatin yanzu a jihar ta aiwatar da ayyuka daban-daban a fadin jihar ba tare da aro ko sisin kwabo daga kowa ba. Bugu da kari, babu wani dan kwangila a jihar da yake bin gwamanti bashi saboda mun tabbatar da cewa yan kwangiloli ba su rasa kudade don su iya kawo ayyuka masu inganci cikin lokacin da aka kayyade.

Gwamnati na za ta ci gaba da aiwatar da ayyukan da suka shafi jama’a domin ci gaban jihar. Don haka, goyon baya da hadin kai daga dukkan ‘yan kasa masu kishin kasa yana da muhimmanci domin dukan jihar ta amfana daga ayyukan ci gaban jiha.

Related Posts

Leave a Comment