Home Labarai Gwamnatin tarayya ta kaddamar da rabon abinci da taki ga Alumman shiyyar Arewa maso yamma 

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da rabon abinci da taki ga Alumman shiyyar Arewa maso yamma 

by masta

A yau ne na samu karramawar na jagoranci taron rabon kayan tallafi na gwamnatin tarayya a yankin Arewa maso Yamma da aka gudanar a Kano.

Wannan shiri, wani muhimmin bangare ne na ajandar sabunta fata na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, da nufin magance kalubalen tattalin arziki da wahalhalun da ‘yan kasa ke fuskanta a fadin kasar nan.

Wannan shirin ba wai don bayar da agajin gaggawa ba ne kawai, amma don karfafa kudirin gwamnati na kyautata rayuwar kowane dan Najeriya.

Rarrabawar a fadin Arewa maso Yamma yana a matsayin muhimmin tsari yayin da muke aiki don kawo tallafin da ake bukata ga al’ummomi masu rauni.

Yayin da muke ci gaba da wannan shiri, ina mika godiyata ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa jagoranci da hangen nesa.

Ina kuma yaba wa kokarin duk masu ruwa da tsaki wajen ganin an gudanar da wannan shiri cikin sauki.

Hakin da ya rataya a wuyan mu shine ganin cewa wadannan kayan aikin sun kai ga wadanda suka fi bukatarsu.

Za mu ci gaba da sadaukar da kai don gina Najeriya mai ci gaba. Da fatan wannan shirin ya kawo sabon fata da kwanciyar hankali mai dorewa ga jama’armu.

Rt Hon Sen Barau Jibril DSP

Related Posts

Leave a Comment