Na yi kira ga jam’iyyar PDP da ta sake tunani kan shawarar da ta yanke na kauracewa zabukan kananan hukumomi masu zuwa da aka tsara za a yi a ranar 21 ga wannan wata. Shugabannin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar (SIEC) an nada su ne daga gwamnatin PDP da ta gabata, kuma ban canza wannan tsari ba.
Ina mamakin dalilin da ya sa PDP ke jin tsoron shiga cikin zabukan da SIEC ta shirya. Ina so in yi amfani da wannan dama don tabbatar wa ‘yan adawa a jihar cewa SIEC, karkashin mulkina, za ta gudanar da zabukan kananan hukumomi masu ‘yanci, adalci, kuma masu inganci. Na yi taro da Shugaban SIEC, kuma ya tabbatar min da sahihin zabe; duk wanda ya ci zabe za a sanar da shi a matsayin wanda ya ci.
Saboda haka, ina kira ga mutanen jihar Sokoto su fito kwansu da kwarkwatarsu su zabi ‘yan takarar jam’iyyarmu ta APC don ci gaba da ayyukan ci gaba na jama’a a jihar Sokoto.
Ba tare da shakka ba, gwamnatin yanzu ta yi fice a dukkan fannoni na ci gaba. Manoma a jihar Sokoto suna jin dadin takin zamani kyauta, magungunan kwari, da sauran kayan aikin gona a matsayin wani bangare na matakan inganta samar da amfanin gona a jihar.
Mun saka fitilun titi wadanda ke amfani da hasken rana masu dimbin yawa a Sokoto, mun gina tituna da dama, kuma mun tabbatar da cewa ma’aikatanmu suna karbar albashinsu daga ranar 19 zuwa 20 na kowane wata, sabanin abin da aka fuskanta a lokacin gwamnatin da ta gabata.


