Home Labarai Uwar gidan gwamnan jihar Katsina Hajiya Zulaihat ta ziyarci karamar hukumar Zango domin kaddamar da duba marasa lafiya gami da basu magani kyauta

Uwar gidan gwamnan jihar Katsina Hajiya Zulaihat ta ziyarci karamar hukumar Zango domin kaddamar da duba marasa lafiya gami da basu magani kyauta

by masta

Kamar yadda na zagaya kananan hukumomi 34 dake fadin jihar Katsina lokacin yakin neman zabe haka zan sake zagayawa domin kyautata rayuwar al’ummar mu musamman mata da kananan yara.

Inji uwar gidan gwamnan jihar Katsina Hajiya Zulaihat Dikko Umar Radda (Giwar Gwagwaren Katsina)

Uwar gidan gwamnan ta fadi haka ne ranar asabar 07-09-2024 lokacin da ta .

Tare da tallafin abinci ga marasa lafiyan da aka duba. Tare da kara bama al’umma tabbacin yin duk abinda ya dace domin kyautata rayuwar su kamar yadda kullum ake bakin kokari.

Shidai wannan shiri aka kaddamar shiri ne da dukkan wani mara lafiya dake fadin karamar zaizo domin a duba shi kuma a bashi a magani a abinda ke damun sa kyauta.

Daga karshe uwar gidan gwamnan ta yi godiya ga mai gidan ta Mal. Dikko Umar Radda bisa kykkyawan shugabancin sa a jihar Katsina, gami da rokon al’umma addu’oin zaman lafiya.

Mutane da dama ne suka gabatar da jawabai gami da yin godiya da fatan alkairi ga uwar gidan gwamnan wanda suka hada da shugaban karamar hukumar Alh. Babangida Yardaje.

Kwamishinan yada labarai na jihar Katsina Dr. Bala Salisu Zango, mai dakin shugaban karamar hukumar Zango da dai sauran su.

Related Posts

Leave a Comment