284
Mai Girma Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf kenan yanzu haka yayinda yake Tarbar Mai Girma Mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Kashim Shettima a babban filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano dake cikin birnin Kano, Akan hanyarsu ta zuwa babbar Makarantar horarwa da yaye sababbin jami’an Hukumar Yan sanda na kasa dake garin Wudil a jihar Kano, inda za a gudanar da bikin yaye sababbin jami’an yan sanda na wannan shekarar.






