Daga Alkalamin Marubuciya Bilkisu Yusuf Ali, Kano
A kwanakin baya gwamnan jihar Sokoto Alh Dr Ahmad Aliyu ya yi wata magana kan haka rijiyar borehole amma adadin kudin da ya fada sai aka yi masa caa aka fara yada farfaganda har abin ya zama abin zolaya ga wadanda suka jahilci mai gwamna yake nufi da abin da gwamna zai yi. Fadin za a yi borehole masu karamin sani sai suka dauka borehole ce irin wanda aka saba yi a gidana da gidanka. Injiniyoyin kirki da yake sana’arsu ce haka borehole ka ji sun yi magana? To ba su ce komai ba saboda sun san borehole kala-kala ce kuma kudi –kudi ce ta danganta da ina za a gina ta da wanda zai gina ta da kuma amfanin da za ta yi. Wato wadanda za su amfana da ita. Bari na ba ku misali.
Borehole irin ta gidanka da gidana in za a yi ta ana haka ta ne ko dai a cikin gida ko a waje kuma ta ba wa cikin gida ruwa da yan fanfuna a kofar gida. Wannan ba za ka hada kudinta da borehole din da za ka yi wanda za ta ba wa unguwa ko gari ruwa ba. Ana borehole din zamani mai aiki da solar da panel. Shi kansa panel din ya danganta daga daya har 100. Bayan panel akwai tankuna na karfe da karafunan da ake dora tankin, duka suma kudi ne wanda kai Mr lay man ba ya cikin tsarin borehole dinka mai karamin karfi. Daga inda za a yi borehole din zuwa inda za a janyo a kai ruwan ka san mita nawa ne? ba ka da wannan adadin amma ka ke jayayya akan kudin? Ba na mantawa a Kano a shekarun baya an taba irin wannan cecekucen akan za a yi borehole a Audu Bako secretariat akan kudi miliyan ishirin da bakwai a ma wancan lokacin kuma ko a lokacin da aka fito da kudin dalla-dalla sai aka ga ma sai an yi ciko, bare a naira irin ta yau ko dala irin ta yau. Hatta a pipe inci -inci ne don haka irin wannan pipe din ana amfani da five inches ne Wanda ba shi ake amfani da shi a irin borehole ta gidaje ba ko masallaci in ana maganar zurfin borehole da za a saka, zurfinsa a borehole da ake yi a gida ba ya fin mita hamsin zuwa sittin kai har me mita arba’in a kuma samu ruwa wanda zai isa bukatun mutanen gidan. Ba za ka hada kudinsa da irin wannan borehole din da gwamnan Sakkwato yake bayani ba wanda za a yi mita dari biyu har zuwa dari hudu a kasa saboda adadin wadanda za su amfana da ruwan da iya nisan da ake son a kai ruwan da kuma karko ko quality na aikin da ake bukata ruwan ya kai don amfanin al’umma. Kada ka manta wurin da za a Yi irin wannan borehole Yana da bambanci, Sokoto kowa yasan tana kusa da Sahara don haka inda za a haka a samu ruwa yana da bambanci da inda za a yi a Kano ko Jigawa ko Bauchi. Hatta motocin da suke haka borehole din sun bambanta da Wadda ake yi a wasu jihohi da garuruwa. Don haka, don an ce za a yi borehole kan 1.2 Billion guda ishirin da biyar bai kamata ya zama abin surutu da ce-ce-ku-ce ba, kamata ya yi a tsaya a ga wanne irin borehole za a yi tukunna. Hatta pump machine za a yi amfani da grundfos submersible pump series five ne AC DC don haka yana da bambanci da Wanda ake amfani da shi yau da gobe a gidaje da unguwa. Don haka ya kamata adawar siyasa da ma wadanda su ba adawar suke ba fatansu kawai su ga kuskure su yada ya kamata su jira. Bahaushe yana cewa “komai gaggawar Ungozoma ta jira dai a haihu” don haka Ahmad Aliyu a dai yanzu yana kan aiki bai yi kuskure ba a fadin za a yi sababbin borehole ne da kudin kuma za a yi masu inganci ne da nisan zango. Da kyakkyawan fatan duk inda matsalar ruwa take in dai wadannan borehole sun tabbata to za a yi sallama da matsalar da yardar Allah. Allah ya sa mu dace, amin.
Gina Borehole a jihar Sakkwato kan 1.2 Billion tsakanin sani da rashin sani
314


