Home Labarai Amb. Bilkisu Yakubu Indabo Ta Ajiye Muƙaminta Na Riƙon Ƙwaryar Ƙaramar Hukuma Da Aikin Ta Na Gwamnati Domin Tunƙarar Zaɓe Don Ɗarewa Kujerar Shugabar Ƙaramar Hukumar Wudil A Jihar Kano.

Amb. Bilkisu Yakubu Indabo Ta Ajiye Muƙaminta Na Riƙon Ƙwaryar Ƙaramar Hukuma Da Aikin Ta Na Gwamnati Domin Tunƙarar Zaɓe Don Ɗarewa Kujerar Shugabar Ƙaramar Hukumar Wudil A Jihar Kano.

by masta

Biyo bayan ayyana aniyarta ta tsayawa takarar shugabancin ƙaramar hukumar Wudil a Jihar Kano, mun samu labarin Ambassador Bilkisu Yakubu Indabo ta ajiye muƙaminta na riƙon ƙwaryar ƙaramar hukumar Wudil da aikin ta na gwamnati domin samun damar shiga fagen takarar zaɓe wanda zai gudana a wannan wata.

Cike da nuna ƙarfin gwuiwa da farin ciki Amb. Bilkisu Yakubu Indabo ta bayyana cewa ta yanke wannan shawara ce domin hakan ne kawai zai iya bata dama wajen aiwatar da ɗaruruwan ƙudirorin alkhairi da ta tsara domin kawowa al’ummar ta cigaba a fannin ilimi, lafiya, noma, tsaro, samarda ayyukan dogara da kai da shauran su.

Hajiya Bilkisu tayi kira ga al’ummar ƙaramar hukumar Wudil da su ɗauki wannan mataki nata a matsayin jihadi da tukuici na irin goyon baya da addu’o’in alkhairi da suke yi mata babu dare babu rana, kuma tayi alwashin cewa zata kasance mai jin koke-koken duk ɗan ƙaramar hukumar Wudil maza da mata, babba da yaro, sannan tayi alƙawarin gudanar da shuwagabanci bisa adalci da riƙon amana ba tareda nuna banbanci ba.

Daga ƙarshe ta miƙa godiya ta musamman ga Mai Girma Engr Rabi’u Musa Kwankwaso, Mai Girma Engr Abba Kabir Yusuf, Mataimakin Gwamna Comrd. Aminu Abdussalam Gwarzo bisa irin soyayya da kauna, da kuma amincewa da ita sukayi don ganin ta bayarda irin tata gudummawar wajen tafiyar da gwamnati da kawo cigaba a ƙaramar hukumar Wudil da Jihar Kano.

Wane fata zaku yi mata?

Related Posts

Leave a Comment