Home Labarai 28 August, 2024 11:04

28 August, 2024 11:04

by masta

MALAM ABDUL’AZIZ ABDUL’AZIZ: SHUGABA TINUBU BAI YI ZAƁEN TUMUN DARE BA

Abdulaziz Abdulaziz, Yana ɗaya daga cikin yan jaridar da suka sadaukar da rayuwar su don su fadakar da al’ummar Najeriya sahihin abinda Ke faruwa musamman akan matsalar tsaro. Akan haka har daji ya shiga, yayi hira da jagoran yan ta’adda, Bello Turji, wanda mutane da yawa suke tsoron haduwa da. Akan haka Ina tunanin har gwamnatin da kake cewa suna tare tasa mashi ido tunanin ko yana da wata alaka ta daban da yan ta’adda. Yau don ya fito yayi bayani kan abinda ya sani ya hanyar bincike mai zurfi, bai dace a watsar da maganar shi don kawai yana yi ma gwamnati mai ci aiki ba. Shi fa maganin matsala daga fahimtar ta yake farawa. Duba kasa Kaga irin yabo da ya samu a lokuta daban daban. Duk kana ganin tarayya da gwamnati tasa ya samu wannan nasarar ko kuwa jajircewa da kuma sanin makamar aiki da kiyaye sharuddan aikin?

https://www.premiumtimesng.com/news/headlines/300092-premium-times-journalist-wins-nigerias-top-investigative-journalism-award.html

https://dailytrust.com/just-in-trust-tvs-abdulaziz-wins-wole-soyinka-awards-for-investigative-reporting/

A haƙiƙanin gaskiya, zaɓo Malam Abdulaziz Abdulaziz a matsayin mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa, ko shakka babu shugaba Tinubu bai yi zaɓen tumun dare ba duba da yadda yake jajircewa kan duk wata dama da ta taso yana ƙoƙarin ganin matasa sun amfana da ita a fannoni daban-daban.

Related Posts

Leave a Comment