295
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya mika ta’aziyya ga al’ummar Masarautar Ningi da gwamnatin jihar Bauchi bisa rasuwar Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya.
A wata sanarwa da ta fito daga fadar gwamnati, Shugaban ya bayyana marigayin sarkin a matsayin hazikin
shugaba da ya yi amfani da mukaminsa wajen yi wa al’umma hidima.
Shugaba Tinubu ya yi addu’ar Allah Ya jikan sarkin, ya kuma bai wa iyalansa da al’ummar Masarautar, da ma Najeriya hakurin rashinsa.
Marigayi sarkin Ningi ya rasu ne a yau ranar Lahadi, 26/Agusta/2024


