Home Labarai Maimartaba Sarkin Ningi da ke jihar Bauchi, Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya, ya rasu, yana da shekara 88.

Maimartaba Sarkin Ningi da ke jihar Bauchi, Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya, ya rasu, yana da shekara 88.

by masta

Sakataren masarautar, Alhaji Usman Sule, Magayakin Ningi, shi ne ya bayyana labarin rasuwar a wata sanarwa, inda ya ce, Allah Ya yi wa Sarkin rasuwa ne yau Lahadi da Asuba a Kano.

Sanarwar ta kara da cewa za a yi jana’izar Sarkin mai daraja ta daya, yau da karfe hudu na yamma a fadarsa da ke Ningi.
An haifi marigayi Alhaji Yunusa Danyaya a shekarar 1936, a garin Ningi kuma ya zama sarki a shekarar 1978.

Related Posts

Leave a Comment