Home Labarai Bikin Naɗin Sarautar Sarkin Malaman Gaya.

Bikin Naɗin Sarautar Sarkin Malaman Gaya.

by Muhsin Tasiu Yau

Mai Martaba Sarkin Gaya Dr Aliyu Ibrahim Abdukqadir (KIRMAU MAI GABAS)
zai naɗa Malam Munzir Sheikh Dr. Yusuf Ali a matsayin Sarkin Malamai na masarautar Gaya a karo na biyu.

Malam Munzir Dr. Yusuf Ali ɗa na ga fitaccen malamin Islama nan dake jihar Kano
Shekh Dr. Yusuf Ali wanda watanni shida baya ya koma ga rahamar ubangiji. Zai gaji mahaifinsa a matsayin wannan sarauta matsayin na biyu a jerin wanda suke wannan sarauta a wannan masarauta mai albarka.

Za’a gudanar da wannnan naɗin ranar juma’a 17/05/2024 a fadar mai martaba sarkin gaya da misalin ƙarfe 10:00pm.

Muna Addu’a Allah ya kama ya sanya alkhairi. Allah ya ƙara jadddawa rahama ga ruhin Sheikh Dr. Yusuf Ali.

 

 

Related Posts

Leave a Comment