Home Labarai Fadar Masarautar Gaya a yau laraba 9/5/2024

Fadar Masarautar Gaya a yau laraba 9/5/2024

by masta

GEMT.

Mai martaba sarkin Gaya Alh (Dr) Aliyu Ibrahim ya tabbatar da nadin digatai Guda uku a yayin zaman fadar yau laraba.

A yayin zaman na yau Mai martaba sarki yaja hankalin Digatan da aka nada wadanda suka hadar da :
Alh. Sunusi Garba Wanda aka nada Digacin Yautar Arewa dake kasar Gabasawa,da Mal. Sule Abubakar shi Kuma Digacin Gumawa a kasar Gabasawa,da Kuma Digacin Indabo Mal. Saminu Abdullahi , dasu zamo masu gaskiya da rikon amana, ya Kuma gargade su, da su gujewa yin Amfani da rawnin su a harkar siyasa,ya Kuma Sha alwashin hukunta dukkan Digacin da aka samu ya hada Kai da 6arayi ko azzalumai wajen cutar da Al’umma.

Daga karshe yayi addu’ar Allah kama.

Allah ya taimaki sarki, ya karawa sarki lafiya. Amen.

Comr. Ubaliyo Falalu Gaya
Mashawarci na musamman ga Sarkin Gaya kan kafafen sada zumunta na zamani
8/5/2024.

Related Posts

Leave a Comment