Home Labarai An Kama ’Yar Sanda Bisa Zarginta da Satar Yara a Sokoto

An Kama ’Yar Sanda Bisa Zarginta da Satar Yara a Sokoto

by Muhsin Tasiu Yau

 

Rundunar yan sandan Abuja ta ceto wasu yara biyar da aka sace daga jihar Sokoto zuwa babban birnin tarayya.

 

Haka kuma an kama wata jami’ar ‘yar sanda, Kulu Dogon Yaro da ake zargi da kitsa shigewa gaba wajen raba yaran da iyayensu.

 

Jaridar Daily Trust ta wallafa, Kulu Dogon Yaro na aiki a bangaren kula da mata da yara a caji ofis din Kubwa da ke Abuja.

 

Ana zargin ‘yar sandan, wacce ‘yar asalin karamar hukumar Zuru ce a jihar Kebbi ce da hada baki da wata Elizabeth Oja da sato yaran daga jihar Sokoto.

 

Kulu da Elizabeth makota ne da ke zaune ne a barikin Mopol da ke Dei-dei a birnin tarayya Abuja, kuma sun dauko yaran a mota daga Sokoton har zuwa Abuja.

 

Gwamnatin jihar Sokoto ta karbi yara biyar daga hannun rundunar ‘yan sandan Abuja baya da aka gano su a birnin, ciki har da masu shekaru biya da shekaru uku, da kuma jaririya ‘yar makonni biyu.

 

Kwamishinan harkokin addini a jihar Sokoto, Dr Jabir Sani Maihula ne ya karbi yaran a madadin gwamnatin jihar.

Related Posts

Leave a Comment