Home Labarai Wasika zuwa ga ‘yan kasuwarmu

Wasika zuwa ga ‘yan kasuwarmu

by masta

1. Assalamu Alaikum, da fatan kuna cikin ƙoshin lafiya da aminci. Allah Ya amintar da mu duka, Amin.

2. Abinda mutanen Najeriya suka sani shine: gwamnati ta yi iya bakin ƙoƙarinta na ganin ta dai daita farashin dala. Wanda a yanzu ta ke akan farashin ₦1400, a gwamnatance.

3. Yanzu da ake wahalar abinci, muna ganin abubuwan mamaki daga gareku. Wasu ƴan kasuwan sai kaje sayen abin ₦1200 da zarar an samu ɗan ƙarin lokuta sai kaji ya koma 2k ƙarin ɗari takwas. Wasu kuma kasuwar tsaye kawai suke ci. Don su samu a saida da tsada.

4. Tabbas akwai masu tausayi cikin ku, waɗanda basa ƙarin farashi mai yawa. Amma kuskuren su shine sun san masu ƙarawa kayansu kuɗi a cikin manyan dillalan manyan ƴan kasuwar kuma suke cin karensu babu babbaka. Don haka su kuma suke cin aladen su babu babbaka! Sai su ƙyale suna sayerwa mutane kaya tsada.

5. A kwanakin baya duk abinda ka taya yau a kasuwa gobe ko an jima idan ka koma sai ka ji an faɗa maka sabon farashi wai saboda dollar ta hau.
Yau fiye da kwana goma da ruguzowar dala daga kusan N1,950 zuwa N1,400 amma shiru kake ji masu son tsawwalawa jama’a ba sa ko niyyar sauƙaƙawa talaka. Da yawansu kuma su ne kan gaba wajen la’antar gwamnati idan abubuwa basa tafiya daidai.

6. An dai yi gangami kawai ana ta kunnawa mutane masifa. An saka mutane a wahala. Gwamnati tana ta bakin ƙoƙarinta akan ta saita komai ya dawo dai dai, Amma ku kun fake sai kuna ta azabtar da ƴan uwanku. Kuma a gefe guda kuna ɗorawa gwamnati laifin bayan laifin naku ne.

7. Ina muku nasiha ku ji tsoron Allah ku dena ƙuntatawa mutane. A matsayin ku na Alhazan. Birni da na Ƙauye, na san kune dai kuke ta ƙoƙarin raba gero da sikari da shinkafa a watan azumi. Wannan aiki ne mai kyau na taimakon mutane, Allah ya bada lada. Amma fa shi kuma tsawwalawa al’ummar Manzon Allah ﷺ babban zunubi ne wanda Manzon Allah ﷺ yayi Allah wadai da shi, kuma yayi addu’ar da zaka iya ƙiranta "Allah Ya isa". Kada ka yarda al’umma ta wahala saboda wani falala wanda Allah Ya maka.

8. Taimakon musulmai ba dole sai da sadakar azumi ba. Yana daga cikin taimakon ƴan uwanka musulmi kayi amfani da damar da Allah Ya baka don kawar musu da wani raɗaɗi da suke fama da shi. Malamin Musulincin nan mai suna Imam Ibnul Qayyim cikin littafin Al-Fawaa’id ya kawo nau’o’i da yawa da aka bi wajen taimakon musulmi don ya fita daga wani ƙunchi na rayuwa.

9. Daga cikin abubuwan, Ibnul Qayyim yace, (ومواساة بالتوجّع لهم ، وعلى قدر الإيمان تكون هذه المواساة فكلما ضعف الإيمان ضعفت المواساة وكلما قوي قويت). Ma’ana, "yana daga cikin taimakon ɗan uwanka musulmi ace, a jikin ka kaima kana jin zafin uƙubar da yake ciki. Kuma shi wannan taimakon kana yin shi ne gwargwadon imanin ka. Mutumin da yake da raunin imani, to zaka ga taimakon da zai bada mai rauni ne. Mutum mai ƙarfin imani kuwa zaka ga ya bada taimako mai ƙarfi.."

10. Daga nan sai malamin ya bada hujjar cewa shi yasa ka ga Manzon Allah ﷺ Ya fi kowa taimakon sahabban sa. Kullun cikin himmar kawar musu da damuwar rayuwar su yake.

11. Yanzu kai da za’a baka Dala daga gwamnati a farashin da ta ke bayarwa a yanzu haka, da yarjejeniyar zaka saida akan farashin da ta ce a sayar, saboda Allah zaka lissafa kanka cikin masu tausayi a lokacin da ake cikin wannan mawuyacin halin, ko kuma a matsayinka na ɗan kasuwa ka fito da farashin da al’umma zasuji daɗi kana saidawa. Kai baka son gina lahirar ka ne da ladan tausayin al’ummar Manzon Allah ﷺ?

12. Allah Ya riga ya hore maka gida, da motar shiga, da kuɗin da ka fi ƙarfin buƙatun ka na rayuwa. To don Allah bayan ka tsawwalawa mutane sun sha wahala ka samu kuɗi, me kake fatan yi da kuɗaɗen? Menene ka kasa iya siya ka ci wanda kake tsammanin zaka iya siyan shi yanzu da ka maƙure al’ummar Manzon Allah ﷺ?

13. Tunda dai Allah Ya baku duniya, da ace zaku lura, to lokaci yayi da zaku fi bada ƙarfi wajen gina lahirar ku. Ku sakewa sauran talakawa mara suyi fitsari su ji sauƙi. Ku ji tausayin su, sai ku ga kuma Allah Ya tausaya muku, Ya kuma albarkaci lamarin ku.

14. Wahalhalun da talaka yake ciki, ƴan kasuwa suna da ikon da zasu iya sa wasu abubuwan suyi ɗan sauƙi. Buri zasu rage. Kuma kamar yadda suke bada sadakar azumi don tausayin talakawa waɗanda talauci ya danne, to lokaci yayi da zasu yi amfani da falalar su wajen sauƙaƙawa mutane wahalu a gidajen mai, da kuma kasuwanni. A bada farashi mai kyau.

15 Ina mana fatan alheri gaba ɗaya. Haza wasalam!

Related Posts

Leave a Comment