AN BAYYANA FARFESA MUHAMMAD ALI PATE A JERIN SUNAYEN MINISTOCI 12 DA SUKA FI ƘOƘARI.
Sakamakon wani rahoton binciken da jaridar Economic Confidential ta fitar a kan ayyukan majalisan zartaswar gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na tsawon watanni takwas, ya ayyana sunayen ministoci guda goma sha biyu (12) cikin guda arba’in da biyar (45), a matsayin wadanda suka fi himma da ƙoƙari wajen tabbatar da samun nasarar shirin gwamnatin shugaban Bola Ahmed Tinubu na sabunta fatar al’ummar Nijeriya wato (Renewed Hope).
Ministan lafiya da kyautata walwalan al’ummar Nijeriya, farfesa Muhammad Ali Pate, ya samu kansa cikin jerin sunayen ministocin guda goma sha biyun ne saboda namijin ƙoƙarinsa na karkato da hankalin abokan hulda irin su GAVI, gidauniyyar Susan Thompson Buffett da sauransu, ya zuwa ga farfado da harkokin kiwon lafiya a Nijeriya, tare da kuma ƙoƙarin Farfesa Muhammad Ali Pate na sanya riga-kafin cutar kansar mahaifa a cikin tsarin riga-kafi ta kasa.
Bugu da kari, jaridar ta bayyana ƙoƙarin Farfesa Pate na samar da yarjejeniyar fahimtar juna da shugaban bankin Afreximbank domin samar da bashin dala biliyan guda. Wanda za’a yi amfani da shi wajen samar da adashen hannayen jari ga kamfanonin zuba jari waɗanda ke da sha’awar zuba jari a wajen samar da masana’antun kiwon lafiya a Nijeriya, wanda zai zama matsayin daya daga cikin dalilan da suka dogara da shi.
Sunan Farfefasa Pate, Ministan lafiya da walwala, shine a sahu na ukku a bisa ga rahoton da jaridar Economic Confidential ta wallafa a shekaran jiya talata 27 ga watan biyun 2024.
*Pate Media Center*


