Katsina Times Photos gallery 📸
Hukumar Hisbah a jihar Katsina ta kai ziyarar sada zumunci da hadin gwiwa don aiki tare a ma’aikatar harkokin mata ta jihar Katsina.
Malam Aminu Usman PhD. (Abu Ammar) babban kwamandan Hisbah na jihar Katsina da tawagar tasa sun samu kyakkyawar tarba daga Kwamishiniyar Mata Hajiya Zainab Musa Musawa.
Zainab Musa Musawa ta bayyana matukar jin dadin ta da goyon bayan hukumar da kuma hada hannu don aiki tare, musamman akan halin da mata suka tsinci kansu na lalacewar tarbiyya cin zarafi da sauransu.
Ziyarar da ta kasance a ranar Talata ta samu rakiyar Shugaban gudanarwa na hukumar, Alhaji Shehu Kankia da Shugaban sashin kudi da sauran ‘yan rakiya daga Kungiyoyin Dariku na Shi’ara’ul Islami, Munazzamatu da sauransu.
Credit
Katsina Times






