
A yau Lahadi babbar tawaggar shehunan Tijjaniyya ƙarƙashin jagorancin Sheikh Mahe Nyass da Sheikh Dahiru Usman Bauchi ta kai ziyara ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
A yayin ziyarar shehunan guda biyu sun yi addu’o’in neman taimakon Ubangiji ga Najeriya da addu’ar Allah ya yi riƙo da hannun shugaba Tinubu domin samar da cigaban da ƙasar ke buƙata.
Sheikh Mahe ya yi kuma kira ga ƴan Najeriya da su dage da addu’a kan halin da ake ciki tare da kuma yin haƙuri da yiwa shugabanni fata nagari.
Ya ce Najeriya ƙasa ce mai albarka kuma uwa a Afirka don haka cigaban ta ko akasin haka zai shafi ƙasashe da dama.
A na sa jawabin Shugaba Tinubu ya yi godiya ga shehinan guda biyu tare da tuna irin addu’o’i da fatan alheri da suka yi masa a yayin da yake yaƙin neman zama shugaban ƙasar Najeriya.
Tinubu ya ƙara jaddada aniyarsa ta bunkasa harkar noma domin samar da wadattacen abinci ga dukkanin al’ummar ƙasa

