Home Labarai Sarkin Gaya Alhaji Dr Aliyu Ibrahim Kirmau Mai gabas ya aurar da ‘ya’yansa guda 5 a fadarsa da ke garin Gaya.

Sarkin Gaya Alhaji Dr Aliyu Ibrahim Kirmau Mai gabas ya aurar da ‘ya’yansa guda 5 a fadarsa da ke garin Gaya.

by masta

Mai martaba sarkin karaye ne Dr.Ibrahim Abubakar ll ya Bada auren "ya"yan sarkin na Gaya Guda biyar ,inda uku daga cikin su "y"Yan sarkin ne na cikinsa,sai Kuma "yar Wamban Gaya Guda daya wadda shi Kuma Yaya ne Mai martaba sarki,da "yar Dan Iyan Gaya Wanda shi Kuma kani ne ga Mai martaba sarkin.

An Gudanar da Taron Daurin auren ne a Babbar fadarsa Dake Garin Gaya,inda Mai martaba sarkin karaye Alh. Dr. Ibrahim Abubakar ll (kyauren yammawa), ya wakilci Bada auren nasu.

Yayin Taron Daurin auren wakilan Mai martaba sarkin Bichi,dana Mai martaba sarkin Rano, wakilan Tsohon sanatan Kano ta tsakiya Dr. Rabi’u Musa kwankwaso,da wakilan Gwamnan jihar kano Eng. Abba Kabir Yusuf, former AIG police academy Wudil, suka halarci Taron,da sauran su.

Anyi addu’ar fatan zaman lafiya da kwanciyar hankali ga Masarauta,jiha da Kuma kasa Baki daya.

Allah ya taimaki sarki, ya karawa sarki lafiya. Amen.

Comr. Ubaliyo Falalu Gaya
Mashawarci na musamman ga Sarkin Gaya kan kafafen sada zumunta na zamani
27/1/2024.

Related Posts

Leave a Comment