Home Labarai Muna son masarautunmu don suna da matukar amfani ga al’ummar jihar Kano

Muna son masarautunmu don suna da matukar amfani ga al’ummar jihar Kano

by masta

*Wasik’a Zuwa ga Wad’anda Abin ya Shafa*

Assalamu Alaikum!

Barka da wannan lokaci, tare da fatan alheri a gare ku da dukkanin masu taimakawa wajen gudanar da mulkin jahar Kano.

Al’umma da dama sun zab’e ku ne saboda kyautata maku zato na cewa za ku yi abubuwan da suka shafi cigaban jahar Kano da kuma samar da walwala da farin ciki a tsakanin al’umma. Ba kun hau wannan mulki don d’aukar fansa da raba kan al’umma ba.

Ku tuna fa, da yawa daga cikin mutanen da suka zab’e ku, suna rayuwa ne a cikin sabbin masarautun nan da aka samar a wannan jaha tamu mai albarka. Da yawa daga cikin wad’annan mutane ba su san me ce masarauta ba, sai a dalilin samar da wad’annan sabbin masarautu. Ba su san ya al’adar hawan Sallah take ba, sai da abin ya zo kusa da su. Wani ma baitaba saka Sarki a idon sa ba.

Samar da wad’annan masarautu, ya haifar da cigaba ta fuskar tattalin arziki da bunk’asa al’adu da samar da walwala a tsakanin al’ummun da ke zaune a wad’annan masarautu.

Mutane da dama ne suka zabe ku, ka da ku biye san zuciyar mutum d’aya, ku b’ata wa miliyoyin mutane.

Lalle ya dace a yi duba na tsanaki ka da a yi aikin da za a zo nan gaba ana da-na-sani. Wad’annan sarakuna hak’ik’ka cigaba ne a Jahar Kano, tab’a su daidai yake da tab’a masoyanku, wad’anda suka fita iya karfinsu, suka tabbatar da cewa kun sami nasara. Haka kuma dai su d’in ne suka yi ta addu’a ba dare ba rana, har Allah ya ba ku nasara a Kotun K’oli (wanda ba dan addu’o’in nan ba da yanzu ba wannan labari ake yi ba).

Akwai kuskure, mu ce duk abin da aka samar a jaha cigaba ne, amma samar da wad’annan masarautu ake kallonsu a matsayin ci baya.

Samar da wad’annan masarautu, ya samar da sabbin hakimai. su kuma wad’annan hakimai sun sama wa mutane da dama hanyar cin abinci. Haka zalika an bunk’asa harkar kasuwanci, domin an samar da yan kasuwa masu sai da kayayyakin al’ada tun daga rawani zuwa manyan riguna. Akwai alkairai da dama a cikin wad’annan masarauta masu albarka.

Kun gaji sarauta, kuma Kun san irin k’ok’arin da iyaye da kakanni suka yi wurin kulawa da mutumcin wannan masarauta. Allah ya saka wa jagora Dr Rabiu Musa Kwankwaso da alkairi ya yi wata magana mai tasiri kwarai yake cewa “lokuta da dama mutum yana kawo wani abu da niyya mummuna, amma a k’arshe sai ta juye ya zama alheri”. Wannan maganar abar dubawa ce kwarai.

Wannan lokaci, ba lokacin da za a zauna ana k’irk’irawa kai makiya ba ne, lokaci ne na k’ara masoya. Fatan mu nan gaba ku k’ara shekaru 7 masu albarka.

Mu tuna a baya fa yawan al’ummar Kano ka’dan ne, wanda a yau mun ninka sama da sau goma. Me ya sa za mu yi tunanin k’arin sarakuna kuskure ne ?

Kada mu manta da sauran makwaftan mu sarakuna nawa suke dasu, Kuma da yawansu Nasu SARAKUNAN sunfi namu daraja. Musali Sarkin sokoto, Gombe, gwandu da Maiduri duk fa gaba suke da Sarkin Kano. Wurin darajar tsarin mulki a kasar hausa. Amma su sunada sarakuna Mai ya same su ?

Idan a baya muna da masallacin idi daya, kasuwa daya, jami’a daya k’ananan hukumomi ‘yan kad’an. Ita kanta jahar Kano d’in a had’e take da Jigawa, amma daga baya aka samar da jahar Jigawar. Hakan bai zama cigaba ba ?

Kusan dükkanın jahohinmu na Arewa suna da mabambanta masarautu wanda hakan ya kawo masu cigaba da bunk’asa tattalin arzkinsu ta b’angarori da dama.

A hangena na mai k’ananan shekaru ya dace gwamnti ta yi duba idan da kurakurai, sai a gyara, wanda ina da tabbacin ba zai dawo da mu baya ba, Kuma kar a yi abin cikin san zuciya, Domin wata rana in mu ne wata rana rana ba mu ba ne.

Wallahi a cikin wad’anda suke amfana da masarautun nan akwai wad’anda masoya ne. Hak’ik’a in an yi duba za a ga cewa idan aka tab’a masarautun nan, su ma an tab’a su.

Wallahi nasan mutumin da a dakin Allah yake adduar samun nasararku a lokacin zabe. Muna magana da shi a yanzu haka hakimi ne a d’aya daga masarautun nan. Idan na ga wani abu a kan masarautun nan, sai n ji kawai na tuna shi, da irin kokari da ya yi na ganin samun nasarar mulkin nan.

Allah ya sani ina ba da shawara ne ba dan wani abu ba, sai don na sauke nauyi a matsayina na mai son cigaban gwamnatin nan.

Haka zalika, ina kira ga wanda yake kwad’ayin sake dawowa karagar mulkin nan da ya tuna da makomar sarautar da kuma duba da irin baiwar da Allah ya yi masa ya hakura ya yi amfani da tauhidin da ya amfani da shi a baya, da ya ce, “Allah ne yake ba da mulki kuma ya gode da ya karb’a”. Ina gudun ka da dawowarka ta zama sanadin rushewar cigaba da bunk’asar tattalin arziki da aka samu a dalilin wad’annan masarautu.

Ina son wannan gwamnti don Allah, kuma ina fatan samun nasara cikin mulkinta.

A k’arshe ina addu’ar Allah ya zab’a mana abin da ya fi alheri ga al’ummar jahar Kano da k’asa baki d’aya.

Nagode
H.I Muhammad Ph.D (In view)

Related Posts

Leave a Comment