Home Labarai Mai martaba Sarkin Gaya Alh Dr Aliyu Ibrahim ya nada hakimai guda uku yau a fadarsa.

Mai martaba Sarkin Gaya Alh Dr Aliyu Ibrahim ya nada hakimai guda uku yau a fadarsa.

by masta

Sarkin Gaya ya Taya Hakiman daya nada murna,da Addu’ar ya kama.

Mai martaba sarkin Gaya Alh (Dr) Aliyu Ibrahim ya tabbatar da nadin Hakimansa Guda uku ,inda aka daga darajar sarautar Alh. Aminu Ibrahim Gaya daga Yarima zuwa Dan Iyan Gaya, Alh. Ghali Ibrahim Khalil aka nada shi sarautar Dan Kaden Gaya, sai Kuma yunusa Aliyu Ibrahim Wanda aka yiwa sarautar Yariman Gaya.

Jim kadan bayan nadin nasu ne Mai martaba sarki ya taya su murna tare da Addu’ar ya kama,ya Kuma ja hankalin su da su zamo masu gaskiya da rikon amana,da Kuma ci gaba da taimakon al’umma.

Ya Kuma yi addu’ar Allah ya bamu lafiya da zama lafiya. Amen.

Comr. Ubaliyo Falalu Gaya
S A Media to the Emir Gaya
26/1/2024.

Related Posts

Leave a Comment