Tinubu shugaba Mai TAUSAYI da TAUSASAWA
A Jawabin da ya gabatar wa ‘yan kasa a ranar daya ga watan Janairun 2024
Shugaban ya bayyana manufofin gwamnatinsa a shekarar 2024 da kuma fadada shirinsa ga ‘yan Najeriya a sabuwar shekara
Shugaban ya fara da waiwaye adon tafiya kan yadda ya zama shugaban kasa har ma ya yaba da mulkin dimokuradiyyar Najeriya na tsawon shekaru 24.
Shugaban Ya kuma tantance nasarorin da ya samu a cikin watanni bakwai da hawansa karagar mulki, inda ya bayyana kokarin da ya yi na hana abin da ya kira bala’in kasafin kudi da ya afka wa Najeriya. Tinubu ya yi magana akan daukan matakai masu wahala da ya yi da suka hada da kawar da tallafin mai da kuma rage yawan ƴan tsirarun da ke yin kafar angulu ga hada-hadar kudi ta Najeriya.
Shugaban ya yarda cewa waɗannan zaɓi biyu sun haifar da rashin jin daɗi ga ‘yan Najeriya, ya roki yan kasar da su amince su kuma yarda da shi akan cewa wahalar da suke ciki ta dan karamin lokaci ce a cewarsa
Muhimman alkawurran da shugaban ya yi wa ‘yan Najeriya a cikin jawabinsa nasa sun
1.Bangaren wutar lantarki
Tinubu yace “A cikin watan Disamban da ya gabata a wajen taron COP28 a Dubai, sun kulla yarjejeniyar gaggauta kammala aikin samar da wutar lantarki na Siemens wanda a karshe zai samar da dauwamammiyar wutar lantarki a karkashin shirin Shugaban Kasa na inganta Wutar Lantarki wanda ya fara a cikin 2018. Baya da wannan ma akwai wasu karin aiyukan samar da wutar da ke gudana a fadin kasar, domin a cewarsa gwamnatin ta fahimci cewa babu wani canjin tattalin arziki mai dorewa da zai samu ba tare da tsayayyen wutar lantarki ba."
2. A bangaren fetur kuwa Shugaban yace Matatar Mai ta Fatakwal da ta Dangote zasu fara samar da tatattacen mai na cikin gida
3. BANGAREN ABINCI Awannan bangaren, shugabaTinubu ya yi alkawarin kara kaimi wajen noma kadada 500,000 na gonaki a fadin kasar nan domin noman masara, shinkafa, alkama, gero, da sauran kayan amfanin gona masu mahimmanci domin tabbatar da samar da abinci, tsaro da kuma rage farashin abinci.inda ya kara da cewa
“tuni muka kaddamar da noman rani mai cin fadin hekta 120,000 a jihar Jigawa a watan Nuwamban da ya gabata a karkashin shirin mu na bunkasa alkama na kasa.”
4. INGANTA HANYOYIN ZUBA JARI, Shugaban ya sha alwashin mayar da Najeriya kasar da za ta fi bayar da shaawar zuba jari a cikin gida da waje a wannan sabuwar shekara, Tinubu ya yi alkawarin kawar da duk wata tangarda da zata iya kawo tarnaki ga hakan ciki har da aiwatar da sauye-sauyen a bangaren kasafin kudi da saukaka haraji
Tinubu ya ce "A duk balaguron da na ke yi zuwa kasashen waje, sakona ga masu zuba jari da sauran ‘yan kasuwa daya ne shine Kofofin Najeriya a bude suke don kasuwanci kowa. Zan kuma yaki duk wani cikas da ke tunkaro harkokin kasuwanci a Najeriya, kuma ba zan yi kasa a gwiwa ba wajen kawar da duk wata tangarda da ke kawo cikas ga hanyarmu ta mayar da Najeriya wurin da za a iya zuba jari a cikin gida da waje" –
5. Tinubu yayi alkawarin aiwatar da fannoni 8 da ya fi bai wa fifiko a cikin kasafin na 2024 wanda suka hada da Tsaro, samar da ayyukan yi, rage talauci, da sauransu. Inda ya ce "A cikin gabatar da kasafin kudin shekarar 2024 ga Majalisar Dokoki ta kasa, na lissafa abubuwa guda 8 da gwamnatina ta fi bai wa fifiko wadanda suka hada da tsaron ciki da wajen kasa. samar da aiyukan yi, kakkabe talauci, Inganta Ilmi, Inganta kananan kasuwancin ‘yan kasa, zuba jari a rayuwar ‘yan kasa, domin lallai mun dauki wadannan matukar muhimmanci"


