Home Labarai Mataimakin Shugaban Kasa da wasu gwamnoni sun Kai wa Shugaban Kasa Ziyara a Lagos, ciki har da gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf

Mataimakin Shugaban Kasa da wasu gwamnoni sun Kai wa Shugaban Kasa Ziyara a Lagos, ciki har da gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf

by masta

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya jagoranci tawagar
Gwamnoni zuwa gidan Shugaban kasa Bola Tinubu don kai masa ziyarar ban girma a gidansa dake Bourdillon ta jahar Lagos inda yake hutun karshen shekara.

Gwamnonin da ke cikin tawagar sun hada da gwamnan jihar Lagos, Sanwo-Olu, Dapo Abiodun na Ogun Biodun Oyebanji na Ekiti AbdulRahman sai
AbdulRazaq na Kwara,.

Sauran sun hada da Gwamna Abba Kabir Yusuf na jahar Kano da Hope Uzodimmar Jahar Imo da Yahaya Bello na Kogi, da Dauda Lawal na jahar Zamfara.
Gwamnonin da madugun tafiyar wato Mataimakin shugaban kasa Kashim sun sami tarba daga Shugaban kasa

Related Posts

Leave a Comment