399
Babbar kotun jihar Bauchi ta daya ta yankewa Adamu Abdulra’uf da Abdulkadir Wada hukuncin daurin shekaru 35 a gidan yari kowannen su, bisa samunsu da laifin yin mummunar illa da yunkurin kashe wata yarinya ‘yar shekara shida.
Bayan sun amsa laifin, Alkalin kotun mai shari’a Rabi Umar ta yanke masu hukunci.

