Shugaban kungiyar Injiniyoyi na duniya ya ziyarci sarkin Gaya. Mai martaba sarkin Gaya Alh (Dr) Aliyu Ibrahim ya kar6i bakuncin shugaban ne Mai suna Eng. Mustapha Balarabe Shehu a yayin zaman fadar yau Litinin a fadarsa Dake Garin Gaya.

by Muhsin Tasiu Yau

Eng. Mustapha yace sunzo fadar ne domin Neman Tabarraki da shawarwari ga Mai martaba sarki. Ya Kara da cewa tun da farko ya fara da shugabancin jiha ne,daga nan ya rikye shugabancin kungiyar ta kasa,kana ya zama shugaban kungiyar na Africa, yanzu Allah ya nufe shi da zama shugaban kungiyar Injiniyoyi na Duniya Baki daya.

 

Ya Kuma yi Godiya da irin addu’o’i da shawarwari Daya samu a gun Mai martaba sarki.

 

Da yake jawabi Mai martaba sarki,yayi matukar farin ciki da wannan matsayi da Allah ya Bashi,Kuma yace” abun farin ciki shi ne kasancewarsa Dan Gaya.” Ya Kuma ja hankalinsa da yayi amfani da damar da Allah ya Bashi ya kawowa kasarsa da jiha harma da garinsa (Gaya) ci gaba.

 

Haka Kuma, kungiyar Nigerian peace Unity and progress karka shin jagorancin kwamandan Malam. Lawan wada, sun kawo ziyarar Neman Tabarraki.

 

Mai martaba sarki,ya yaba musu, ya Kuma hore su da kauracewa nuna 6angaranci a harkar aikinsu.

 

Makarantar Hayyakallah Islamiyya school Dake Darmanawa karamar Hukumar Tarauni jihar kano,sun kawo ziyara da Neman sa Albarka,inda cikin jawabin shugaban kungiyar Iyayen yara Mal. Zakariyya ya roki Mai martaba sarki Daya kasance a matsayin Mai Gayyata yayin Gudanar da Taron saukar Qur’ani Mai Girma nan gaba kadan.

 

Mai martaba sarki,ya amsa tare da tabbatar da  Goyon bayansa,ya Kuma umarce su da Bada muhimmanci wajen kula da tarbiya.

 

Daga karshe, shugabancin kungiyar sha’irai (Ahbabu) na Garin Gaya karka shin jagorancin shugabanta Malam. Naziru Yakubu Gaya,sunzo ne domin Neman amincewar sarki da Kuma goyon bayansa kan tabbatar da Daina sakin dukkan Wani bege har sai an tace shi,domin gujewa afkawa 6arna.

 

 

Mai martaba sarki,yaji dadi sosai tare da bada goyon bayansa kan wannan lamari,har ila yau ya Sanya musu albarka bisa wannan dogon Hange da suka yi .

 

Yayi addu’ar Allah ya bamu lafiya da zama lafiya. Amen.

 

Comr. Ubaliyo Falalu Gaya

S.A Media Gaya Emirate

11/12/2023.

Related Posts

Leave a Comment