972
An Yanke Ma Wanda Ake Tuhuma Da Yima Almajiri Fyade Hukuncin Daurin Rai Da Rai.

Wata babbar kotun jihar Jigawa da ke zamanta a Birnin Kudu a ranar Alhamis ta yankewa wani matashi dan shekara 25, Israfilu Sagiru da ke kauyen Zarena a karamar hukumar Birnin Kudu hukuncin daurin rai da rai bisa samunsa da laifin fyade.
An gurfanar da wanda ake tuhumar ne a ranar 5 ga Satumba, 2021, a gaban babbar kotu a kan tuhumar aikata laifuka biyu na fyade da ake yi masa na lalata da almajirai biyu masu shekaru 11 da 12.
Da yake yanke hukunci, Mai shari’a Musa Ubale ya ce masu gabatar da kara daga ma’aikatar shari’a ta jihar, sun tabbatar da dukkanin shaidu.
Ya ce laifin ya sabawa sashe na 3 (1) (e) na dokar hana cin zarafin mutane (VAPP) mai lamba 02, 2021.




