A cikin wani faifen bidiyo da aka yaɗa a shafin ‘X’ (Tiwita a da) na gidan talabijin na Channels TV, Mista Rotimi Amaechi, fitaccen ɗan siyasa, tsohon gwamnan Jihar Ribas kuma tsohon Ministan Sufuri a gwamnatin da ta gabata, ya yi wata magana mai zafi game da tunanin masu zaɓe a Nijeriya.
Kalaman Amaechi sun nuna abin da yake ganin tamkar rashin tunani ne a tsakanin ’yan Nijeriya dangane da mutuncin ’yan siyasar ƙasar, inda ya ce, duk ’yan ƙasar na matuƙar zargin ’yan siyasa da zama ɓarayin gwamnati, amma ba su fasa zaɓen su ba.
Ya bayyana ra’ayinsa kamar haka; “a bayyane ta ke cewa, ’yan Nijeriya sau da yawa sun tabbatar da aniyar ‘yan siyasa. Shin kun taɓa haɗuwa da wani ɗan siyasa a fili ya yarda cewa ya yi almundahana?
“’Yan Nijeriya sun san irin waɗannan abubuwan, amma duk da haka, su na cigaba da kaɗa ƙuri’unsu na goyon bayan waɗannan ’yan siyasa. Don haka, dole na tambaya; me ya sa ku ke cigaba da aiwatar da hakan?”

