Home Labarai Ministoci mata na Tinubu suna bayyana jiki kamar masu takarar sarauniyar kyau, inji ministan Buhari

Ministoci mata na Tinubu suna bayyana jiki kamar masu takarar sarauniyar kyau, inji ministan Buhari

by Muhsin Tasiu Yau

Tsohon Ministan Sadarwa a gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, Adebayo Shittu ya soki ministoci mata a majalisar ministocin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, inda ya bayyana cewa su na saka sutura tamkar ’yan takara sarauniyar kyau.

Shittu ya bayyana ra’ayinsa ne a yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels, inda ya jaddada muhimmancin jami’an gwamnati su tunkari ayyukansu da muhimmanci.

Shittu, wanda ya yi aiki a ƙarƙashin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari daga 2015 zuwa 2019, ya yi waɗannan kalamai ne a matsayin martani ga jawabin da shugaba Tinubu ya yi wa ministocinsa.

Yayin buɗe taron kwana uku na ministoci da mataimakan shugaban qasa, Tinubu ya yi gargaɗin cewa zai tsige duk ministan da bai tsaya ya yi aiki tuƙuru ba.

Game da gargaɗin shugaban aasar kuwa, Shittu ya bayyana cewa, “Na ji daɗin yadda shugaba Tinubu ya naɗa mata ministoci da dama, amma idan na gansu a talabijin, sai a ga kamar an yi musu ado ne na gasar saraunkya kyau.”

Sannan ya kuma jaddada buaatar dukkan ministocin su nuna jajircewarsu wajen gudanar da ayyukan gwamnati, ya kuma buaaci gwamnatin APC da ta nuna da gaske wajen gudanar da ayyukanta.

Related Posts

Leave a Comment