Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe
Jarumar Hausawan Duniya, Hajiya Talatu Suleiman ‘Yar Nijeriya, ta yi kira ga gwamnatin Nijeriya da cewa a gaggauta kawo ƙarshen satar ɗaliban sakandare da ya zama ruwan dare a yankin Arewacin Nijeriya.
Hajiya Talatu ‘Yar Nijeriya ta yi wannan kiran ne a lokacin wani taron manema labarai da ta kira inda ta ja kunnen gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, da cewa ba za su lamunci yawan kai hare-hare da ake yi makarantun sakandare ana sace ɗalibai mata ba.
Ta ce a matsayinta na uwa kuma Basarakiya a Ƙungiyar Hausawa ta Duniya shi ya sa ta fito ta shaida wa duniya cewa yawan sace ɗaliban yana ɗaga musu hankali domin hakan na nuni da cewa kamar da wata manufa ake yi domin ‘yan Arewa kawai ake sacewa.
A cewarta tana wannan maganar ne da muryar Hausawa domin yin shiru ba zai yiwu ba shi ya sa ta kira taron manema labarai domin isar da kukansu ga Shugaban Nijeriya da masu ruwa da tsaki a harkar da ta shafi tsaro.
“Rashin ɗaukar mataki don kawo ƙarshen satar ɗaliban zai sa mu fito tituna mu yi zanga-zangar nuna rashin jin daɗin mu kan abinda ke faruwa,” inji ta.
Ta ce Hausawa ne suka fi zaɓar shugaban ƙasar har ya ci zaɓe to don me ya sa ba za a kawo ƙarshen sace musu ‘ya’ya ba.
Har ila yau Talatu ‘Yar Nijeriya ta ce abinda takaici sai a sace ɗaliban a shiga da su daji ana keta musu ‘yanci, hakan na nuni da cewa karatun ‘ya’ya matan ne ba a so kenan.
Ta ci gaba da cewa idan har ba a samu canji ba nan da wani lokaci kaɗan za su tara jama’a zuwa Majalisar Dattawa ta Ƙasa don gabatar da kukan su har sai an saurare su an kuma yi musu alƙawarin za a ɗauki mataki.
“Za mu rubuta koken mu zuwa Majalisar Ɗinkin Duniya da ta shiga tsakani wajen tsawatarwa Shugaban Nijeriya don kawo ƙarshen sace mana ‘ya’ya da bai faruwa a kudancin ƙasar sai a Arewa.”
A ɓangaren bautar da ƙananan yara kuma ‘Yar Nijeriya ta ce za su haɗa kai da ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam wato human right da hukumar yaƙi da safarar al”umma don yaƙi da bautar da yara ta hanyoyin da ba su dace ba.
Ta ce za su yi dukkan .ai yiwuwa wajen ganin duk masu hannu wajen safara ko bautar da ƙananan yara da sunan aikatau an hukunta su.
Sannan ta ce yaran sune manyan gobe kuma su ake bi ana sacewa kuma ba wani mataki da aka ɗauka don kare ci gaba da sace su.
Daga nan sai ‘Yar Nijeriya ta ce hatta irin iyayen nan da suke fakewa da talauci suna bada ‘ya’yan su don aikatau za su sa a hukunta su domin ya zama izina ga masu irin wannan halin.

