Home Labarai Ma’aikatan lantarki sun umarci mambobinsu su janye ayyukansu bayan jikata shugaban NLC

Ma’aikatan lantarki sun umarci mambobinsu su janye ayyukansu bayan jikata shugaban NLC

by Muhsin Tasiu Yau

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ma’aikatan wutar lantarki a ƙarƙashin Ƙungiyar Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Ƙasa (NUEE) sun buƙaci mambobinsu da su dakatar da dukkan ayyukansu a faɗin ƙasar nan da tsakar daren Alhamis.

Ƙungiyar ta ce ta ɗauki matakin ne domin nuna rashin amincewarta da kama tare da cin zarafin da ‘yan sanda suka yi wa Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya, Joe Ajaero a ranar Laraba a wani gangamin zanga-zanga a Owerri, babban birnin jihar Imo.

Biyo bayan harin da jami’an tsaro suka kai wa Ajaero a jihar Imo, NLC ta ce shugabannin qungiyoyin ƙwadagon za su yi wani taron gaggawa nan ba da daɗewa ba domin ɗaukar matsaya mai muhimmanci kan lamarin.

Shugaban sashen yaɗa labarai na ƙungiyar NLC, Benson Upah, wanda ya zanta da THISDAY ta wayar tarho a ranar Alhamis, ya ce za a kira taron dukkan ɓangarorin ƙungiyar domin duba matakin da ‘yan sanda da gwamnatin jihar Imo suka ɗauka a yayin zanga-zangar da NLC ta shirya a Owerri.

Ya ce duk wata ƙungiya mai alaƙa da ita tana da ‘yanci a cikin doka don ɗaukar duk wani mataki na nuna rashin jin daɗin ta da lamarin Owerri.

Sai dai a wata wasiƙa mai taken: ‘Tattaunawa don Yajin aikin sai baba-ta-gani na ilahirin ƙasar saboda sace Shugaban NLC, Joe Ajaero’, ƙungiyar ta bayyana a matsayin rashin tausayi da rashin mutuntawa da aka yi wa Ajaero wanda ya zama Babban Sakataren NUEE.

Wasiƙar da aka aike wa dukkanin sassan ƙungiyar mai ɗauke da sa hannun mataimakin babban sakataren ƙungiyar, Dominic Igwbuike, ta bayyana cewa: “A matsayin martani ga mummunar aika-aikar da aka yi wa ɗan uwanmu shugaban ƙungiyar NLC da gwamnan jihar Imo da ‘yan sandan jihar suka yi. Rundunar ‘yan sandan jihar Imo a yau Laraba, 1 ga watan Nuwamba, 2023, za mu fara shirin rufe ƙasa baki ɗaya idan ba a saki shugaban ƙungiyar ba tare da bayar da cikakken bayani daga gwamnatin Nijeriya.

“Don haka, an buƙaci dukkan shugabanni na ƙasa, jihohi da su fara haɗa kan mambobinmu don bin umarnin gaba ɗaya.

“Don Allah a lura cewa janye ayyukan zai fara ne a faɗin ƙasar da ƙarfe 00.00 na ranar Alhamis, 2 ga Nuwamba, 2023.

“Ba za mu iya zama a wurin aiki ba yayin da Shugaban NLC ke tsare kuma ba za mu iya samun zaman lafiya ba yayin da ake tauye haƙƙin ma’aikata a jihar Imo ba tare da wani hukunci ba.”

Da alama dai an aiwatar da wannan umarni ne a Jihar Imo a ranar Alhamis, 2 ga Nuwamba, inda ilahirin jihar ta kasance cikin duhu.

Related Posts

Leave a Comment