Home Labarai Ministan Labarai ya buƙaci ‘yan Nijeriya su mara wa burin Tinubu baya don farfaɗo da ƙasa

Ministan Labarai ya buƙaci ‘yan Nijeriya su mara wa burin Tinubu baya don farfaɗo da ƙasa

by Muhsin Tasiu Yau

Ministan Labarai da Wayar da Kan ‘Yan Ƙasa, Mohammed Idris, ya ce tun da yanzu Kotun Ƙoli ta yanke hukunci, kamata ya yi ‘yan ƙasa a haɗe kai sannan a mara wa burin farfaɗo da ƙasa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke da shi.

Ministan ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai a Abuja biyo bayan hukuncin Kotun Ƙoli na tabbatar da nasarar da Shugaba Tinubu ya samu a babban zaɓen 2023.

Ya ce shari’a ta wuce, yanzu lokaci ne da ɗaukacin ‘yan Nijeriya za su haɗa kai wajen ciyar da ƙasa gaba.

Ya ce tun bayan da Shugaban Ƙasa ya kama aiki aiki ran 29 ga Mayu, aike yake babu kama hannun yaro don tabbatar da burinsa na farfaɗo da Nijeriya, wato Renewed Hope Agenda.

Ya ƙara da cewa gwamnati na sane da halin matsin da ‘yan ƙasa ke ciki sakamakon cire tallafin mai da aka yi wanda tuni tana ɗaukar matakin rage wa ‘yan ƙasa raɗaɗin.

Daga nan, Ministan ya zayyano shirye-shiryen da gwamnatin Tinubu ta shirya za ta yi amfani da su domin cire ‘yan ƙasa daga ƙunci.

Related Posts

Leave a Comment