Home Labarai ‘Yan sanda sun cafke babban wanda ake zargi da kashe matar aure a Borno.

‘Yan sanda sun cafke babban wanda ake zargi da kashe matar aure a Borno.

by Muhsin Tasiu Yau

Rundunar ‘yan sanda a jihar Borno, a ranar Talata ta ce ta saki mijin matar da aka kashe a gidan aurenta da ke Maiduguri bayan ta kama babban wanda ake zargi.

Rundunar ‘yan sandan ta ce an sako mijin marigayiyar, mai suna Adamu Ibrahim da abokinsa, Bukar Wadiya da aka tsare su bayan sun kai rahoton afkuwar kisan ga ‘yan sanda.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta hannun mai magana da yawunta ASP Sani Kamilu.

Ya ce an bi sawun babban wanda ake zargin, Abacha Bukar tare da kama shi da laifin kisan matar mai suna Fatima Alhaji-Bukar mai shekaru 24 a ranar 18 ga watan Oktoba.

Kamilu ya ce ‘yan sanda sun kama wanda ake zargin ne bayan da suka bibiyi wayar marigayiyar da ya sace.

Ya ce an kuma kama wasu mutane biyar da ake zargi da karɓar sauran kayayyakin da aka sace a yayin kisan da kuma haxa kai wajen aikata laifi.

A cewarsa, sauran waɗanda ake zargin sun haɗa da Ibrahim Mustapha, Usman Yusuf, Muhammed Yunus, Nuhu Mohammed da Ismaila Mohammed Barka duk a yankin Gwange na Maiduguri.

Related Posts

Leave a Comment