Home Labarai Ƴan bindiga sun kashe mutum tara tare da yin awon gaba da wasu da dama a Katsina

Ƴan bindiga sun kashe mutum tara tare da yin awon gaba da wasu da dama a Katsina

by Muhsin Tasiu Yau

Wasu mahara ɗauke da muggan makamai da ake kyautata zaton ɓarayin daji ne sun hallaka mutum tara, gami da yin garkuwa da wasu mutane da dama a qaramar hukumar ɗan Musa da ke jihar Katsina.

Wani mazaunin garin da aka sakaya sunansa, ya bayyana wa MANHAJA cewa maharan waɗanda ba zai iya ƙiyasta yawansu ba, sun afka wa garin cikin daren ranar Lahadi da misalin ƙarfe 8:00 na dare.

A cikin mutane tara da suka rasa rayukansu sakamakon harin, har da ɗan sanda da kuma tsohon kantoma na ƙaramar hukumar, wato Hon. Dauda Lawal Mai Iyali.

‘Yan bindigar dai sun yi nasarar tserewa da kayan abincin da suka sata wanda suka bi gida-gida suna karvewa daga hannun jama’a, sun kuma yi awon gaba da mutane da dama waɗanda ya zuwa haɗa wannan rahoton ba a gama tantance adadinsu ba.

Kazalika, ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar, Aminu A. Garba, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda majalisar dokokin jihar ta yi Allah wadai da harin tare da umurtar vangaren zartarwa da ya gaggauta ɗaukar mataki kan lamarin.

Related Posts

Leave a Comment