Nijeriya na shirin rage yawan harajin da gwamnatin tarayya da na jihohi ke karɓa daga sama da 60 zuwa ƙasa da 10, shugaban kwamitin sake fasalin harajin ne ya bayyana hakan a ranar Talata.
Za a ɓullo da sabon tsarin a wani ɓangare na sauye-sauyen da za a samu wajen gudanar da harkokin kasuwanci cikin sauƙi da kuma ƙara samun kuɗaɗen shiga.
Nijeriya, ƙasar da ta fi kowacce ƙarfin tattalin arziki a nahiyar Afirka, tana da kaso 10.8 cikin 100 na haraji da GDP, wanda ɗaya ne daga cikin ƙasashe mafiya ƙarancin wannan adadin a duniya, lamarin da ya tilasta wa gwamnatin kasar dogaro da rancen kuɗi domin gudanar da kasafin kuɗin ƙasar.
Masu zuba jari sukan yi la’akari da yawan karvar haraji a Nijeriya da kuma yawan hukumomin tattara kuɗaɗen shiga da wajen yin lissafin yawar tsadar yin kasuwanci da kuma yin ɗari-ɗari da saka hannun jari.
Taiwo Oyedele, mai bai wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan sake fasalin haraji, ya shaida wa manema labarai cewa, Nijeriya na da sama da haraji da nau’ukan haraji 60 a hukumance waɗanda gwamnatocin tarayya da na jihohi da ƙananan hukumomi ke karɓa, da doka ta wajebta.
Ciki har da harajin da ba na hukuma ba, harajin da hukumomi ke karɓa bisa ƙa’ida ko waɗanda ba sa bisa ƙa’ida, ba ba tare da goyon bayan doka ba. Nijeriya na da nau’ukan haraji sama da 200, in ji Oyedele, inda ya ƙara da cewa wannan adadi mai yawa yana sanya rayuwa cikin wahala.
“Gwargwadon yawan haraji, a gaskiya ma, gwargwadon ƙarancin kuɗaɗen shiga da ake iya tarawa, saboda kawai yana janyo salwantar wasu kuɗaɗen, da kuma wasu mazambata da ba na gwamnati ba suna karvar kuɗi don amfanar kansu,” inji shi.
Oyedele ya ce wani ɓangare na garambawul ɗin zai ga sauye-sauye masu nasaba da kundin tsarin mulkin ƙasar domin fayyace ko wace hukumar gwamnati ce ya kamata ta karɓi haraji iri kaza.
Bila Tinubu

