Daga ISAH GIDAN BAKKO a Zariya
A ranar Asabar da ta gabata, cibiyar horas da kuratan sojoji da aka fi sani da’ Depot Nigerian Army” da ke Zariya ta ƙyanƙyashe kuratan sojoji har 6,315 karo na 85.
A jawabinsa wajen bikin kammala horas da sojojin, babban kwamandan sojojin Nijeriya Laftana Janar Taoureed Lagbaja ya ja kunnuwan kuratan da aka yaye da su zama sojoji nagari a duk inda aka tura su aiki a ciki da wajen Nijeriya.
Laftana Janar Lagbaja ya kuma ce rundunar sonojin Nijeriya da ya ke yin shugabanci za ta ƙara tashi tsaye na ganin ta qara bunƙasa kayayyakin koyo da koyar da ayyukan soja, ya ce an yi wannan yunƙuri me domin ƙara Samar da ƙwararrun sijoji da za su fuskanci ƙalu -balen tsaro da ke addabar Nijeriya a yau.
Da ya ƙara koma wa ga sabbin kuratan sojojin kuma ya yi karatun baya na yadda takwarorinsu kurata da aka yaye su karo na 84 sun nuna bajinta da hali nagari da kuma kishin ƙasa a wuraren da aka tura su domin aiki sojan da aka koya ma su a tsawon lokacin da suka kasance a wannan bariki da aka kafa a shekara ta 1904.
Ya ci gaba da jawo hankalin kuratan da su rungumi kishin ƙasa da juriya da biyayya da kuma kare ɗaukacin ‘yan Nijeriya baki ɗaya ba tare da batun jinsi ko kuma sa addini a wajen aiwatar da ayyukan da aka ɗora su a kai ba.
Lafatana Janar Lagbaja ya kuma ce rundunar rundunar sojojin Nijeriya za ta bunƙasa duk wani batu na kiwon lafiya a cibiyoyin kiwon lafiya da na sojoji da suke Nijeriya, ya ce za a yi haka ne, domin ƙara kula da sojojin Nijeriya a duk wata matsala ta kiwon lafiya da suke addabar sojojin Nijeriya.
A ƙarshen jawabinsa, ya sara wa jami’an wannan runduna na yadda suke sadaukar da kansu wajen horas da kuratan sojoji da suke amsa sunansu na sojoji a ciki da wajen Nijeriya, ya ce ya na fatan za su ruɓanya ayyuka tuƙurun da suke yi, domin wannan cibiya ta ci gaba da amsa sunan ta ta yaye ƙwararrun sojoji da suka yi suna a sassan duniya ba Nijeriya kawai ba.
Shi ko gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani a zantawar da manema labarai jim kaɗan bayan kammala bikin yaye kuratan, ya yaba mahukuntan wannan cibiya na yaye sojojin da suke ilimim ayyukan soja da za su runguma a wannan rana.
Gwamna Uba Sani ya kuma yaba wa rundunar sojojin Nijeriya na yadda suke bayar da gagarumin gudunmuwa na matsalolin ƙamfar tsaro da suke addabar sassa daban-daban na jihar Kaduna da kuma Nijeriya baki ɗaya.
Wannan bikin yaye sojijin ya samu wakilcin Mai Martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli bisa jagorancin Fagachin Zazzau Alhaji Umar Mohammed da kuma Hakimin Sabon Gari Ɗan Barcin na Zazzau Alhaji Ahmed Bashari Aminu da kuma masana ilimi da suka fito daga cibihoyin ilimi a sassan Nijeriya.

