Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayyana cewa yana maraba da hukuncin da Kotun Ƙolin Najeriya ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a John I. Okoro ta yanke kan ƙarar zaɓen shugaban ƙasa da ‘yan takarar jam’iyyar PDP da na Labour suka shigar, inda suke ƙalubalantar hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa.
”Kotun ta yi adalci ga dukkan batutuwan da aka gabatar domin tantance su a cikin ƙorafe-ƙorafen da suka shafi doka, ba tare da tsoro ko fargaba ba.” A cewar Tinubu
“Ko shakka babu, bisa hukuncin yau, ya nuna cewa tsarin zaɓen ƙasar nan da dimokuradiyyarmu sun sami cigaba mara musaltuwa, saboda ƙwazon Alkalai da suka jagoranci lamarin suka nuna wajen yin hukunci na adalci wanda babu son kai a cikin sa”.
Tinubu ya ce “A yau an sake tabbatar da cewa jam’iyyata mai mulki ta APC, ta samu ‘yancin kai da adalci ga ‘yan Najeriya, wanda tun daga lokacin ne na jagoranci wannan ƙasa mai girma a cikin ruɗani na sauye-sauyen da ba a taɓa ganin irinsa ba a ƙasarmu."
"Tare da ɗinbun godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki, na amince da nasarar shari’a a yau tare da tsananin nauyi da tsananin sha’awar fuskantar manyan ƙalubalen da ke fuskantar mutanenmu."
"Nasarar da aka samu a yau ta ƙara ƙarfafa niyyata na ci gaba da yi wa ɗaukacin ‘yan Najeriya hidima ba tare da la’akari da bambamcin siyasa, ƙabila, ko addini ba, sannan zamu zama masu mutunta ra’ayoyin al’umma don samar da kyakyawan Najeriya."
Tinubu ya yi alkawarin jaddada kokarin sa don samar da ci gaba a Najeriya kuma yace zai ci gaba da yin aiki daga safiya zuwa dare, a kowace rana, don gina Najeriya.
Shugaban kasa Bola Tinubu yace “Dukkanmu ‘yan gida ɗaya ne, kuma a wannan lokacin muna buƙatar mu ci gaba da aiki don gina ƙasarmu tare."
“A cikin kwanaki da watanni masu zuwa, na yi imanin cewa za a ɗaukaka kishin ƙasa wajen tallafa wa gwamnatinmu don inganta rayuwar ‘yan Najeriya. A shirye nake in yi maraba da gudummawar da duk ‘yan Najeriya ke bayarwa don haɓakawa da ƙarfafa ci gabanmu tare.”
"Ina mika godiya ta ga ɗaukacin ’yan Najeriya kan aikin yi wa kasarmu hidima. Na sake yin alƙawarin tsayawa tsayin daka wajen samar da ayyuka da shugabanci nagari." Inji Tinubu.
https://www.facebook.com/100003777033423/posts/2853652088103998/?mibextid=UXglBzUGR4uSUZqd


