Home Labarai Zargin Kisan Kai: Kotu Ta Umurci ‘Yan Sanda Su Kawo Shugaban Karamar Hukumar Batagarawa

Zargin Kisan Kai: Kotu Ta Umurci ‘Yan Sanda Su Kawo Shugaban Karamar Hukumar Batagarawa

by Muhsin Tasiu Yau

Alhaji Bala Garba Tsanni

 

 

Kotun Majistare ta 3 da ke zaman ta a jihar Katsina ta umurci ‘yan sanda da su gabatar da shugaban karamar hukumar Batagarawa, Alhaji Bala Garba Tsanni a gaban kotu a ranar 27 ga Nuwamba, 2023, kan zargin kisan kai.

Alkalin kotun mai shari’a Abdulkarim A. Umar ne ya bayar da wannan umarni a zaman kotun da ke Katsina.

Majiyar jaridar Taskar Labarai ta ruwaito cewa an gurfanar da shugaban karamar hukumar Alhaji Bala Garba Tsanni da wasu mutane 11 a gaban kotu bisa zargin kisan hakimin kauyen Dabaibayawa, Marigayi Alhaji Dikko Ahmad.

An gurfanar da wadanda ake tuhumar a gaban kotu bisa zargin hada baki da garkuwa da mutane da kuma kisan hakimin kauyen.

An gurfanar da su ne a karkashin sashe na 59, 249, da 189 na dokar hukunta manyan laifuka ta Katsina.

Related Posts

Leave a Comment