322

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne da suka addabi jihar Kaduna sun kai hari a wani masallaci a kauyen Ga Allah Babba da ke kusa da Sabon Layi a karamar hukumar Birnin-Gwari a jihar.
Majiyar jaridar Taskar Labarai ta tattaro cewa harin da maharan suka kai da sanyin safiyar Talata ya kai ga rasa ran babban limamin masallacin da wasu masu ibada guda biyu.
An tattaro cewa akalla wasu masu ibada biyu sun samu raunuka yayin harin.
Wani mai suna Zubair Abdurrauf, wanda ya tabbatarwa da gidan talabijin na Channels TV cewa lamarin ya faru ne a lokacin da ake gudanar da sallar asuba.

