876
Gwamnatin jihar Katsina Ta Ƙaddamar Da Tallafi Ga Manyan Limamai, Masu Kiran Sallah
Gwamnatin jihar Katsina ta samar da alawus-alawus na musamman ga daukacin manyan Limamai na masallatan Juma’a da mataimakansu da masu kiran Sallah a fadin jihar.
Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana haka a lokacin da yake kaddamar da kwamitin kula da harkokin tsaro na kananan hukumomi talatin da hudu na jihar wanda ya gudana a gidan gwamnatin jihar.
Gwamna Umaru Radda ya ce an dauki matakin ne domin zaburar da malaman addinin su hada kai wajen yaki da rashin tsaro.

