Home Labarai Gwamnati ta jaddada ƙudirinta na bai wa fannin tsaro cikakken goyon baya.

Gwamnati ta jaddada ƙudirinta na bai wa fannin tsaro cikakken goyon baya.

by Muhsin Tasiu Yau

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Nijeriya ta jaddada ƙudirinta na bai wa sojojin ƙasar cikakken goyon baya don ci gaba da kare ƙasa da ‘yan ƙasa.

Hakan ya fito ne daga bakin Ministan Tsaro, Badaru Abubakar, sa’ilin da ya ziyarci Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa, a Babban Ofishin Tsaro da ke Abuja.

Da yake jawabi yayin ziyarar, Ministan ya yaba wa sojojin Nijeriya dangane da nasarorin da suke samu a fagen yaƙi da matsalolin tsaron da ƙasar ke fuskanta.

Ya ce, sojoji na yin bakin ƙoƙarinsu wajen kare ƙasa ba tare da bayyana irin nasarorin da suke samu ba.

Abubakar ya ƙara da cewa, sojoji sun taɓuka matuƙa gaya wajen bai wa ɓangaren samar da mai kariya, ya ce yana da ƙwarin gwiwar sojojin za su ƙara himma wajen bai wa ɓangaren cikakkiyar kariya har komai ya koma daidai kamar yadda yake a baya.

“Ana bai wa bututan mai kariya yadda ya kamata,” in ji shi.

A nasa ɓangaren, Janar Christopher Musa, ya yaba wa Ministan game da irin kulawar da sojoji ke samu daga gwamnati, kana ya buƙaci a ƙara yawan kason kuɗin da ɓangaren tsaro ke samu, bai wa jam’iai horo, kyautata walwalar sojoji da sauransu.

Daga nan, ya sha alwashin sojoji za su mara wa gwamnati mai ci baya, tare da yin kira ga masu ruwa da tsaki a zaɓen gwamnonin da zai guda nan gaba kaɗan a wasu jihohi, da a tabbatar da komai ya tafi daidai ba tare da samun wani cunkoso ko yamutsi ba.

Related Posts

Leave a Comment