Home Labarai Wazirin Fika ya riga mu gidan gaskiya.

Wazirin Fika ya riga mu gidan gaskiya.

by Muhsin Tasiu Yau

Daga BASHIR ISAH

Allah Ya yi wa Wazirin Fika kuma tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Alhaji Adamu Fika, rasuwa.

Sanarwar rasuwar ta fito ne daga bakin Ɗanburan Fika, Alhaji Idris Adamu Kukuri, kamar yadda ya shaida wa majiyarmu ta waya.

Ya ce za a sanar da yadda jana’izarsa za ta kasance bayan an tattauna da Sarkin Fika, Alhaji Muhammadu Abali.

Majiya ta kusa da marigayin ta ce, marigayin ya rasu ne a cikin daren da ya gabata inda ya bar duniya yana da shekara 90.

Wani na kusa da ahalin marigayin, Hassan Gimba Ahmed, ya ce, “Ya rasu ne a hanyar dawowa da shi gida daga Turai inda ya je jinya, Allah Ya sa Aljannatul Firdausi makoma.”

Marigayi Adamu Fika dattijon ƙasa ne mai marbata a idon duniya, wanda ya bada gudummawarsa ga cigaban ƙasa a halin rayuwarsa.

Related Posts

Leave a Comment