Home Labarai Sojoji Sun Kashe Fitaccen Shugaban ‘Yan Bindiga A Bauchi.

Sojoji Sun Kashe Fitaccen Shugaban ‘Yan Bindiga A Bauchi.

by Muhsin Tasiu Yau

Rundunar Sojin Najeriya ta 33 ta bayyana cewa sun yi nasarar kawar da shugaban wasu gungun ‘yan bindiga da suka addabi mazauna karamar hukumar Ningi a jihar Bauchi.

Dan ta’addan mai suna Ya’u ya gamu da ajalinsa ne a wani harin kwantan bauna da sojoji suka yi musu a wata babbar hanyar wucewa a Burra, Ningi, ranar Juma’a.

Rahotanni sun nuna cewa Ya’u shi ne shugaban ‘yan kungiyar da suka yi kaurin suna wajen amfani da manyan makamai a tsakanin mazauna garin Burra.

Related Posts

Leave a Comment