349
Gwamnati ta na duba yadda za ta kara adadin mutanen da za su amfana da tsarin rabon kudi domin rage radadin talauci a Najeriya. Wani dogon rahoton jaridar Punch ya ce ana so a cusa sunayen ‘yan fansho da wasu tsofaffin sojoji a jerin wadanda za a rika rabawa kudi a wata.
Duk wani wanda bai da lambar NIN ta shaidar zama ‘dan kasa da lambar BVN ta banki ba zai samu kudin da bankin CBN zai fara rabawa ba.
Kai-tsaye babban bankin zai rika raba kudin daga makon gobe, ba ta hannun wasu ba. Hikimar amfani da NIN da BVN shi ne a bankado sunayen bogi da aka cusa, kuma a tabbatar da cewa kudin zai je ga wadanda aka nufa.

