Home Labarai An cafke wasu shugabannin makaranta kan zargin kashe ɗalibi ta hanyar lakaɗa masa duka a Kaduna.

An cafke wasu shugabannin makaranta kan zargin kashe ɗalibi ta hanyar lakaɗa masa duka a Kaduna.

by Muhsin Tasiu Yau

Hukuma ta tsare shugaban makaranta da mataimakinsa na makarantar Al-Azhar da ke Zaria a Jihar Kaduna bisa zargin kashe wani ɗalibin makarantar mai suna Marwanu Nuhu Sambo hanyar lakaɗa masa duka.

Ana zargin su biyun da hannu a horo mai tsanani da aka ce sun bai wa ɗalibin ɗan ajin JSS3 wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwarsa a ranar Juma’a, 20 ga Oktoban, 2023.

Bayanai sun ce marigayin Sambo ya ci duka a hannun shugabannin makarantar da ma wasu shugabannin ɗaliban makarantar saboda rashin zuwa aji.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan, ya tabbatar da faruwar hakan inda ya ce, “Lallai ‘yan sanda na da masaniya kan lamarin, kuma muna bincike.”

Ya ƙara da cewa, “An kama wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a lamarin. Kuma Kwamishinan ‘yan sanda ya bada odar gudanar da cikakken bincike a kan batun, za mu zurfafa bincike.”

Related Posts

Leave a Comment